Gwamnatin Kano ta yi gargaɗi kan zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini

Hukumar kula da cututtuka ta jihar Kano KNCDC ta fitar da sanarwar gargadi ga ƴan jihar dangane da rahoton da hukumar kula da cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta bayar kan wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini a Abuja.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukan sada zumuntarta.
KNCDC ta ce wannan gargaɗi na daga cikin shirin kare lafiyar al’umma, duba da yadda Kano ke da yawan jama’a da kuma hulɗar kasuwanci da tafiye-tafiye zuwa sauran sassan ƙasar.
Sanarwar ta tabbatar da cewa binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar ba su da cutar Ebola.
Duk da haka, ana ci gaba da gwaje-gwaje domin gano ko cututtuka irin su zazzaɓin Lassa ko zazzaɓin Dengue ne suka haddasa alamomin da aka gani.
