Ɗaya daga cikin matasan Mubi da Gwamnatin Adamawa ta kama ya rasu a gidan yari
Gwamna Fintiri
Umar Abubakar, ɗaya daga cikin mutum 42 da aka kama a Mubi, Jihar Adamawa, ya rasu a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2026, a gidan gyaran hali na Yolde-Pate da ke Yola.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne kwanaki kaɗan kafin ranar aurensa, lamarin da ya jefa iyalansa da amaryarsa cikin alhini.
An ruwaito cewa Umar ya faɗi a gaban kotu a ranar 30 ga Satumba, inda ya nemi beli bisa dalilan rashin lafiya, amma ba a amince da buƙatarsa ba.
Har zuwa rasuwarsa, ba a bayyana cikakken bayani kan irin kulawar lafiya da aka ba shi ba.
A ranar 23 ga Yuli, 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Yola ta ayyana kama mutanen 42 da ci gaba da tsare su a matsayin haramtacce, tare da bayar da umarnin a sake su bisa wasu sharuɗɗa.
Sai dai daga baya, gwamnatin Jihar Adamawa ta sake buɗe wasu sabbin shari’o’i a kansu.
Mutuwar Umar ta haifar da damuwa, inda iyalansa ke kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano ainihin musabbabin rasuwarsa da tabbatar da adalci.
Har yanzu ana buƙatar ƙarin bayani kan yanayin mutuwarsa da kulawar lafiya da ya samu kafin rasuwarsa.
