Zaɓen 2027: Atiku zai gudanar da Gangamin yaƙin neman zaɓe zuwa dukkan Jihohin Najeriya – ADC
Zaɓen 2027: Atiku zai gudanar da Gangamin yaƙin neman zaɓe zuwa dukkan Jihohin Najeriya - ADC
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar ADC ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, zai gudanar da gangamin neman goyon bayan jama’a a dukkan jihohi 36 na ƙasar gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na hukumar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE News, inda ya ce babu wata jiha da za a bari a baya.
Shaibu ya bayyana cewa gangamin ba zai tsaya ga manyan biranen jihohi da tarukan siyasa kawai ba, domin Atiku zai gudanar da tarukan tattaunawa da jama’a, ziyartar al’ummomi, ƙananan hukumomi da wasu ƙauyuka domin jin ƙorafe-ƙorafen al’umma da fahimtar halin da suke ciki.
Ya ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin gangamin nan ba da jimawa ba, domin jama’a su san lokacin da ɗan takarar zai kai ziyara yankunansu.
Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa Atiku zai fi mayar da hankali kan yankin Arewa, yana mai cewa matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da yunwa matsaloli ne da suka shafi al’ummar Najeriya baki ɗaya.
A cewarsa, halin da talaka ke ciki a jihar Zamfara ba shi da bambanci sosai da wanda ke fuskantar ƙalubalen rayuwa a Legas, don haka ADC na da yakinin cewa saƙon Atiku zai isa ga masu zaɓe a dukkan sassan ƙasar.
Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan tarukan gangamin jam’iyyar APC a jihohin ƙasar ba, saboda bukatar haɗa harkokin mulki da ayyukan neman zaɓe.
Sai dai hukumar yaƙin neman zaɓen ADC ta nuna kwarin gwiwar cewa kai tsaye da jama’a a dukkan jihohi zai taimaka wa Atiku wajen neman goyon bayan masu zaɓe, duk da cewa nasarar da yake hasashe za a tabbatar da ita ne ta hanyar sakamakon zaɓen.
