Pantami ya yi barazanar tona asirin masu koƙarin hana shi zama Gwamnan Gombe
Pantami ya yi barazanar tona asirin masu koƙarin hana shi zama Gwamnan Gombe
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi barazanar bayyana sunayen mutanen da yake zargi da ƙoƙarin kawo cikas ga burinsa na zama gwamnan Jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027.
Pantami, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, ya samu tikitin takarar gwamnan Gombe na PDP a ranar 26 ga Mayun 2026.
Pantami ya bayyana cewa ba zai bari wasu mutane su dakile burinsa na siyasa ba, yana mai cewa binciken da aka gudanar ya tabbatar masa da zargin da ake yi na yunƙurin kawo ƙarshen tafiyarsa ta siyasa.
Sai dai takararsa ta fuskanci ƙalubale bayan da wani ɗan takarar fidda gwani na jam’iyyar, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya shigar da ƙara a kotu, lamarin da ya kai ga soke zaɓen fidda gwani na farko da kuma gudanar da sabon zaɓe wanda Pantami ya sake lashewa.
A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon ministan ya bayyana cewa an kashe kuɗaɗe da ƙoƙari mai yawa domin dakile tafiyarsa ta siyasa, amma ya ce zai bayyana sunayen waɗanda yake zargi tare da bayanan abubuwan da suka aikata.
Ya kuma gode wa magoya bayansa bisa addu’o’in da suke yi masa a masallatai da majami’u, yana mai kira gare su da kada su karaya ko su bari sukar da ake yi musu ta raunana musu gwiwa.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 ba tare da sunan Pantami ba, duk da cewa a baya ta sanya shi cikin jerin ’yan takarar gwamnan Gombe. Tawagar lauyoyinsa ta buƙaci hukumar ta dawo da sunansa cikin jerin, tana mai cewa ya cika sharuddan takara.
Sai dai har yanzu makomar takararsa na fuskantar rashin tabbas, yayin da Pantami ya dage cewa masu ƙoƙarin hana shi takara ba za su hana abin da Allah ya ƙaddara ba.
