Hukumar Kwastam ta kwace kayan Fasa-kwauri na Naira miliyan ₦79.8 a jahohin Adamawa da Taraba
Hukumar Kwastam ta kwace kayan Fasa-kwauri na Naira miliyan ₦79.8 a jahohin Adamawa da Taraba
Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Najeriya (NCS), reshen Adamawa da Taraba, ta sanar da kwace kayayyakin fasa-kwauri da darajarsu ta kai naira miliyan 79 da dubu 856 da 500 a cikin makonni biyar.
Mai kula da rundunar, Kwanturola MA Tako, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Yola, inda ya ce jami’an sun samu nasarorin ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da sa ido kan hanyoyin da ake bi wajen safarar kayayyakin haram.
Daga cikin kayayyakin da aka kwace akwai jarkokin man fetur mai lita 25 guda 673, kwatocin sabulun wanka na ƙasashen waje guda 501, buhunan shinkafa daga ƙasashen waje guda 266, da kuma damin tsofaffin tufafi guda 11 tare da manyan buhuna biyar.
Haka kuma, jami’an sun ƙwace wata motar Mitsubishi Canter da ake amfani da ita wajen safarar kayayyakin fasa-kwaurin.
Rundunar ta ce daga cikin ayyukan da ta gudanar akwai gano kwatocin sabulun da aka shigo dashi daga waje guda 451 da aka ɓoye a dajin da ke gefen Kogin Benue, da kuma jarkokin man fetur guda 374 a hanyar daji ta Sahuda, da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Haka kuma, jami’an sun tare motar da ke ɗauke da buhunan shinkafa guda 116 da kwatocin sabulu 50 a hanyar Wuro Alhaji zuwa Maiha, tare da gano wasu kayayyakin da aka shirya fitarwa ta haramtattun hanyoyi.
Kwanturola Tako ya ce an gudanar da kwace kayayyakin ne bisa tanade-tanaden dokar hukumar Kwastam ta shekarar 2023, tare da yabawa Kwanturola-Janar na hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, da jami’an da suka gudanar da ayyukan.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ake zargi da fasa-kwauri, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwar jama’a da kafafen yaɗa labarai na da muhimmanci wajen kare tattalin arzikin ƙasa da tsaron iyakokin Najeriya.
