Faransa ta tabbatar da bullar cutar Shamonda a jikin mutum karon farko a duniya

0
Faransa ta tabbatar da bullar cutar Shamonda a jikin mutum karon farko a duniya

Faransa ta tabbatar da bullar cutar Shamonda a jikin mutum karon farko a duniya

Spread the love

Hukumomin lafiya a ƙasar Faransa sun tabbatar da gano cutar Shamonda a jikin mutum a karon farko a duniya, bayan da wani majiyyaci da ke fama da mummunar rashin lafiyar da ta raunana garkuwar jikinsa ya kamu da cutar, daga bisani kuma ya rasu a farkon watan Oktoba.

Ma’aikatun lafiya da aikin gona na ƙasar sun bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu rahoton gano cutar a jikin ɗan Adam, duk da cewa ta daɗe tana yawo a tsakanin dabbobi a wasu sassan Afirka da Asiya.

Cutar Shamonda na daga cikin cututtukan da suka fi shafar dabbobi, musamman shanu, kuma tana yaɗuwa ne ta hanyar cizon ƙananan ƙwarin da ke ɗauke da ita.

Hukumomin Faransa sun bayyana cewa ana zargin majiyyacin ya kamu da cutar ne sakamakon cizon irin waɗannan ƙwari a gabashin ƙasar, inda aka samu alamun yaɗuwar cutar a tsakanin dabbobi a lokacin bazara da damina ta shekarar 2026. Sai dai bincike kan yadda majiyyacin ya kamu da cutar na ci gaba da gudana.

Duk da rasuwar majiyyacin, hukumomin lafiya sun jaddada cewa, bisa bayanan da ake da su a halin yanzu, ba a gano wata barazanar lafiya ga sauran al’umma ba.

Sun kuma bayyana cewa lamarin na iya kasancewa na musamman, sakamakon tsananin raunin garkuwar jikin majiyyacin, wanda ke karɓar magani saboda wata babbar rashin lafiya.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Turai (ECDC) na aiki tare da hukumomin Faransa da sauran ƙasashen Turai domin tantance yiwuwar illar lamarin ga lafiyar jama’a.

An fara gano cutar Shamonda ne a Najeriya a tsakiyar shekarun 1960, kafin daga bisani a riƙa samun rahotannin kamuwarta a dabbobi a wasu ƙasashen Afirka da Asiya.

A shekarar 2026, an kuma gano cutar a wasu ƙasashen Turai, ciki har da Jamus, Switzerland da Faransa.

Hukumar Lafiyar Dabbobi ta Duniya (WOAH) ta bayyana cewa har yanzu babu allurar rigakafin cutar da ake sayarwa a kasuwa, yayin da masana ke ci gaba da gudanar da bincike domin fahimtar yadda ta iya shafar mutum da kuma hanyoyin da za a bi wajen dakile yaɗuwarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *