Wani Kamfanin ba da shawara a Amurka ya yi zargin Gwamnati na shirin kashe Atiku Abubakar

0
Atiku ga Tinubu: “Zargin ’yan adawa da haddasa yunwa kauce wa gaskiya ne Alhali kai ne ke riƙe da Mulki”

Atiku ga Tinubu: “Zargin ’yan adawa da haddasa yunwa kauce wa gaskiya ne Alhali kai ne ke riƙe da Mulki”

Spread the love

Wata kamfanin ba da shawarwari kan manufofi da hulɗar siyasa da ke Amurka, mai suna Von Batten-Montague-York, ta yi zargin cewa akwai wani shiri na kashe tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Kamfanin ya bayyana cewa rayuwar tsohon mataimakin shugaban ƙasar na iya kasancewa cikin haɗari, duk da cewa ba a gabatar da cikakkun bayanan da za su tabbatar da zargin ba.

Kamfanin, wanda ke da alaƙa da ayyukan hulɗar siyasa na Atiku a Amurka, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira barazanar da ka iya shafar tsaron ɗan siyasar, wanda ake sa ran zai taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu ‘yan adawa, yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

A baya, kamfanin ya sha yin kalamai kan batutuwan siyasar Najeriya da kuma abin da yake ganin barazana ce ga dimokuraɗiyya da ‘yancin ‘yan adawa.

Sai dai, ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu cikakkun bayanai masu zaman kansu da za su tabbatar da zargin shirin kashe Atiku ba.

Don haka, ana buƙatar hukumomin tsaro su gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, idan akwai sahihiyar hujja, domin tabbatar da gaskiyar zargin da kuma kare rayuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *