Jita-jitar da ake yadawa kan komawa na Jam’iyyar APC ba gaskiya bane – Tambuwal

0
Jita-jitar da ake yadawa kan komawa na Jam’iyyar APC ba gaskiya bane - Tambuwal

Jita-jitar da ake yadawa kan komawa na Jam’iyyar APC ba gaskiya bane - Tambuwal

Spread the love

Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar (ADC) domin komawa jam’iyyar (APC) gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Rahoton Daily Post na ranar 19 ga Oktoba, 2026, ya bayyana cewa Tambuwal ya yi watsi da rahotannin da ke alakanta shi da shirin komawa jam’iyyar APC, inda ya fayyace matsayinsa kan jita-jitar da ke yawo game da makomarsa ta siyasa.

Tambuwal, wanda ya taba zama kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya kuma gwamnan Sakkwato na tsawon shekaru takwas, ya koma ADC ne a watan Maris na 2026 bayan ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ya ce sun raunana jam’iyyar.

Batun makomar Tambuwal ta siyasa na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke shirye-shiryen zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai ƙara zafafa fafatawa tsakanin jam’iyya mai mulki da ‘yan adawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *