Tsohon Gwamnan Delta, Emmanuel Uduaghan, ya rasu yana da shekaru 71 kaman yadda iyalansa suka sanar
Tsohon Gwamnan Delta, Emmanuel Uduaghan, ya rasu yana da shekaru 71
Tsohon gwamnan jihar Delta, Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, ya rasu yana da shekaru 71 a duniya. Iyalansa ne suka sanar da rasuwarsa a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, inda suka bayyana alhininsu kan babban rashi da suka yi.
A cikin sanarwar da iyalan suka fitar, wadda Toju Anire Uduaghan ya sanya wa hannu, sun bayyana marigayin a matsayin uba, ɗan’uwa da dattijo mai muhimmanci wanda rayuwarsa ta shafi mutane da dama a jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.
Kafin zama gwamna, Uduaghan ya riƙe muƙamin kwamishinan lafiya na jihar Delta daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan ya zama sakataren gwamnatin jihar daga 2003 zuwa 2007.
Daga bisani, ya zama gwamnan jihar a shekarar 2007, inda ya jagoranci jihar na tsawon wa’adi biyu har zuwa shekarar 2015.
Iyalan marigayin sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.
