Gwamna Fintiri ya sasanta Fulani Makiyaya da Shugabannin Song, inda ya buƙace su da su koma Kasuwa

0
Gwamna Fintiri ya ce Adamawa ta zama jiha mai goyon bayan Tinubu 100% inda ya yi hasashen nasarar APC a 2027

Gwamna Fintiri

Spread the love

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sasanta al’ummar Fulani makiyaya da shugabannin ƙaramar hukumar Song bayan wani saɓani da ya haifar da kaurace wa kasuwar Song da makiyayan suka yi.

Taron sasanta rikicin, wanda gwamnan ya kira, ya gudana ne a ranar Lahadi a gidan gwamnatin jihar da ke Yola.

Rikicin ya samo asali ne daga rashin fahimta tsakanin makiyayan da shugaban ƙaramar hukumar Song, Hon. Idris Yahaya.

Lamarin ya sa makiyayan suka kaurace wa kasuwar, abin da ya kawo tsaiko ga harkokin kasuwanci da mu’amalar al’umma a yankin.

A yayin taron, Gwamna Fintiri ya roƙi ɓangarorin biyu da su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su fifita zaman lafiya da ci gaban ƙaramar hukumar Song.

Ya buƙaci makiyayan da su koma kasuwa tare da zama lafiya da sauran al’umma, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban tattalin arziki.

Sai dai gwamnan ya gargaɗi duk wanda zai ɗauki doka a hannunsa da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba, musamman kashe-kashe da sauran ayyukan rashin bin doka.

A ƙarshen taron, ɓangarorin biyu sun amince su rungumi zaman lafiya tare da komawa harkokinsu na yau da kullum domin amfanin al’ummar Song baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *