Gwamnatin Tinubu ta ce ba za ta dawo da tallafin Man Fetur ba duk da wahalar rayuwa
Bafarawa ya kafa wa Tinubu Sharaɗin samun zaman lafiya kafin ya samu kuri’unsa a 2027
Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan cire tallafin man fetur, duk da matsin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Gwamnatin ta ce ba ta da shirin komawa tsohon tsarin tallafin man fetur ko tsarin canjin kuɗaɗen waje mai farashi daban-daban.
Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana hakan yayin tarurrukan Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya a Bangkok, Thailand.
Ya ce gwamnati na da niyyar ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin da ta fara, duk da tambayoyin da ake yi kan yiwuwar dawo da tallafin.
Oyedele ya kuma bayyana cewa rangwamen da Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) ya yi na tsawon kwanaki 30 ba dawo da tallafin man fetur ba ne, sai dai matakin kasuwanci da aka ɗauka domin rage farashin mai ta hanyar rage ribar kamfanin. Ya ce wannan mataki ba ya nufin gwamnati ta sauya matsayinta kan cire tallafin.
Wannan matsaya ta gwamnati na zuwa ne yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar man fetur, sufuri, abinci da sauran muhimman buƙatun rayuwa.
Duk da cewa gwamnati na ganin gyare-gyaren za su taimaka wajen inganta tattalin arziki, ana ci gaba da kira gare ta da ta ɗauki matakan da za su rage wa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arziki.
