Jakadan Najeriya a Turkiyya ya miƙa takardun shaidar Jakadanci ga Shugaba Erdoğan

0
Jakadan Najeriya a Turkiyya ya miƙa takardun shaidar Jakadanci ga Shugaba Erdoğan

Jakadan Najeriya a Turkiyya ya miƙa takardun shaidar Jakadanci ga Shugaba Erdoğan

Spread the love

Jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya, Sa’idu Usman Nasamu Dakingari, ya miƙa takardun shaidar jakadancinsa ga Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, a wani biki da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar da ke Ankara.

Wannan mataki ya tabbatar da karɓuwarsa a hukumance a matsayin wakilin Najeriya a ƙasar.

Dakingari na cikin jakadu biyar da suka miƙa takardun shaidar jakadancinsu ga Erdoğan a ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026. Sauran sun fito ne daga Indiya, Mali, Netherlands da El Salvador.

A yayin bikin, jakadun sun gabatar da jami’an ofisoshin jakadancinsu da iyalansu ga shugaban Turkiyya, kafin su ɗauki hotunan tunawa da shi. Daga bisani, Erdoğan ya gana da kowane jakada daban-daban.

Ana sa ran sabon jakadan Najeriya zai mayar da hankali wajen ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Turkiyya, musamman a fannonin kasuwanci, ilimi da haɗin gwiwa a muhimman al’amuran ƙasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *