Kungiyar ASUU reshen jami’ar TSU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

0
Kungiyar ASUU reshen jami'ar TSU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Kungiyar ASUU reshen jami'ar TSU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Spread the love

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Taraba (TSU), ta ayyana shiga yajin aikin gama-gari ba tare da sanya ranar ƙarewa ba, saboda gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da ƙungiyar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba za ta janye yajin aikin ba har sai an cika yarjejeniyar da aka cimma, lamarin da ka iya kawo tsaiko ga harkokin karatu a jami’ar, ciki har da koyarwa, jarabawa da sauran ayyukan ilimi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ɗalibai ke buƙatar ci gaba da karatunsu, yayin da rashin daidaito tsakanin ƙungiyar da gwamnati zai iya tsawaita zaman ɗalibai a gida idan ba a samu mafita cikin gaggawa ba.

Ya zuwa yanzu, babu cikakken bayani kan lokacin fara aiwatar da yajin aikin ko matakan da mahukuntan jami’ar da gwamnati za su ɗauka domin warware rikicin. Haka kuma, ba a bayyana ko an fara sabbin tattaunawa tsakanin ɓangarorin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *