Direban da ke gudun VIO ya kashe mata mai ciki a Jos
Direban da ke gudun VIO ya kashe mata mai ciki a Jos
Wata mummunar hatsari ta girgiza al’ummar Jos da ke Jihar Plateau bayan wani direba da ake zargin yana gudun jami’an (VIO) ya kashe wata mata mai ciki har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da direban ke kokarin tserewa daga jami’an VIO cikin gudun tsiya, lamarin da ya jawo rasa ikon sarrafa motarsa.
Shaidun gani da ido sun ce motar ta bugi matar mai juna biyu mai suna Ruth Nen Maurice, inda ta mutu nan take sakamakon munanan raunukan da ta samu.
Mutuwar matar ta jefa iyalanta da mazauna yankin cikin jimami da alhini, yayin da mutane da dama suka bayyana takaicinsu kan yadda direbobi ke gudun jami’an tsaro ba tare da la’akari da rayukan jama’a ba.
Lamarin ya haddasa fushi a tsakanin mazauna yankin, inda wasu suka yi kira ga hukumomi su dauki tsauraran matakai domin dakile irin wannan hatsari da ke janyo asarar rayuka.
Wasu kuma sun bukaci jami’an kula da ababen hawa su rika gudanar da aikinsu cikin tsari domin kaucewa haddasa irin wadannan munanan abubuwa.
Hukumomi sun tabbatar da fara bincike kan abin da ya faru, yayin da ake kokarin gano cikakken bayani game da direban da ya haddasa hatsarin.
