Tinubu zai kaddamar da yaƙin neman zaɓensa da jahar Kaduna ranar 24 ga Oktoba

0
Tinubu zai kaddamar da yaƙin neman zaɓensa da jahar Kaduna ranar 24 ga Oktoba

Tinubu zai kaddamar da yaƙin neman zaɓensa da jahar Kaduna ranar 24 ga Oktoba

Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a jihar Kaduna, a ranar 24 ga Oktoba, kamar yadda Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana.

Yari ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya yi masa bayani kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen da kuma jadawalin ziyarar da shugaban ƙasar zai kai jihohin Najeriya domin neman goyon bayan masu zaɓe.

Ya ce za a gudanar da taron farko na kwamitin yaƙin neman zaɓen a ranar 14 ga Oktoba a zauren taro na fadar shugaban ƙasa, kafin a fara yaƙin neman zaɓen a hukumance a Kaduna.

Ya ƙara da cewa bayan Kaduna, tawagar za ta wuce Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, sannan ta zarce Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Da yake magana kan damar Tinubu na sake lashe zaɓe, Yari ya nuna kwarin gwiwar cewa shugaban ƙasar na da goyon baya a Arewa da Kudu, yana mai cewa samun gagarumin rinjaye a yanki guda ba ya wadatar wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *