Majalisar dattawa ta dage taron tsaro na kasa saboda hatsarin jirgin NAF

0
Majalisar dattawa ta dage taron tsaro na kasa saboda hatsarin jirgin NAF

Majalisar dattawa ta dage taron tsaro na kasa saboda hatsarin jirgin NAF

Spread the love

Majalisar Dattawan Najeriya ta dage taron koli kan tsaron kasa da aka shirya gudanarwa a ranakun 12 da 13 ga Oktoba 2026, saboda mummunan hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya NAF da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ai da ma’aikatan jirgin.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa kuma shugaban kwamitin shirya taron, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da taron bayan kammala tarukan jin ra’ayoyin jama’a daga shiyyoyi daban-daban, sai dai hatsarin ya tilasta dage shi har sai wani lokaci.

Hatsarin ya afku ne a yankin Igbokoda da ke karamar hukumar Ilaje a Jihar Ondo, inda jirgin NAF kirar ATR-42 ya yi hatsari.

Rahotannin da aka wallafa sun ce babu wanda ke cikin jirgin da ya tsira, yayin da ake ci gaba da kokarin gano gawarwaki da tarkacen jirgin.

Matakin Majalisar Dattawa ya biyo bayan ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin karrama jami’an da suka rasa rayukansu.

Majalisar ta mika sakon ta’aziyya ga Shugaban kasa, Rundunar Sojin Sama da iyalan wadanda suka mutu, tare da cewa za a sanar da sabuwar ranar gudanar da taron daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *