Shugaban APC na Edo ya yi barazanar amfani da AK-47 kan masu adawa da tazarcen Tinubu
Shugaban APC na Edo ya yi barazanar amfani da AK-47 kan masu adawa da Tinubu
Shugaban APC na Jihar Edo, Jarrett Tenebe, ya jawo cece-kuce bayan wani faifan bidiyo da ya yadu, inda ya yi barazanar amfani da kalmar “AK-47 fire” kan duk wanda ya yi kokarin hana jam’iyyar samun kuri’un da take shirin bai wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Tenebe ya ce APC na da burin samun kuri’u miliyan 2.5 a Jihar Edo domin Tinubu, yana mai cewa ya kamata magoya bayan jam’iyyar su kara kaimi wajen ganin an cimma wannan buri.
Ya kuma danganta yawan kuri’un da batun samar da sabbin kananan hukumomi da jihohi, yana cewa yawan kuri’un da al’umma ke fitarwa na da muhimmanci wajen samun irin wadannan abubuwa.
Sai dai kalaman da ya yi na ambaton amfani da bindiga sun jawo cece-kuce, musamman ganin yadda ake kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.
