Sojojin Najeriya sun cafke wanda ake zargi da yiwa ISWAP leken asiri a Gombi
Dakarun rundunar Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar mafarauta da ‘yan banga sun cafke wani da ake zargi da yi wa ƙungiyoyin ta’addanci leken asiri a ƙaramar hukumar Gombi, Jihar Adamawa.
Wanda ake zargin, Abdullahi Umar, mai shekaru 25 ɗan asalin Gwoza, an kama shi ne a ranar 23 ga Maris bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ISWAP da Boko Haram a yankin Bataliya ta 232.
Binciken farko ya nuna cewa an tura shi ne domin leƙen hanyoyin shiga sansanin sojoji da wasu muhimman wurare, da nufin shirya kai hare-hare a gaba.
Haka kuma, ya amsa hannu a wani hari da aka kai wa dakaru a Ngoshe.A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da tsare shi domin ƙarin bincike da ɗaukar matakan da suka dace.
