Dangote ya sake kara farashin Fetur a Najeriya

0
DANGOTE-REFINERY-1-1024x576
Spread the love

Matatar mai ta Dangote ta sake kara farashin fetur a Najeriya, inda sabon farashin ya tashi zuwa kusan ₦1,245 kan kowace lita, tare da karin da aka ce ya kai kusan ₦1,275 cikin kankanin lokaci.


Rahotanni sun nuna cewa karin farashin na da alaka da tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma karin kudin aiki.


Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, wanda masana ke ganin zai kara tsananta rayuwa ta fuskar sufuri da kayan masarufi.


Masu lura da al’amuran tattalin arziki sun gargadi cewa ci gaba da karin farashin fetur na iya kara hauhawar farashi (inflation) a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *