Ƙungiyar ƙasashen Musulmai na son a sako mutanen da aka sace a Zamfara

0
20260224_152154
Spread the love

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi Allah-wadai da kisan gillar fararen hula da satar mata da yara da aka yi a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya, a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewa “wannan hari na ƴanbindiga na da muni matuƙa kuma ya saɓa wa dukan ka’idojin ɗan adam.

“Ta ƙara da cewa “ƙungiyar ta nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Najeriya da mutanen ƙasar, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, da fatan Allah ya ba waɗanda suka ji rauni lafiya.

“Ƙungiyar ta buƙaci a sako mata da yara da aka sace ba tare da wani sharaɗi ba, domin dawo da su gida lafiya,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta sake jaddada cewa “dukan ayyukan ƴanbindiga ba za su taɓa samun goyon bayan ƙungiyar ba,” kuma za ta ci gaba da tallafawa ƙasashen membobinta wajen yaki da irin waɗannan mummunar annoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *