An nada Tunji Disu a matsayin sabon Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya cire Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun.
An maye gurbin Egbetokun da AIG Tunji Disu, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
Rahotanni sun bayyana cewa an cire Egbetokun biyo bayan umarnin Tinubu na yin murabus.
An tattaro cewa Tinubu ya umurci Egebtokun da ya yi murabus a wani taro da aka yi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Litinin.
Tinubu ya nada Egebtokun a matsayin Sufeto Janar na 22 a ranar 19 ga Yuni, 2023.
