Farashin kayayyaki ya ragu a Najeriya zuwa kashi 15.10%
Farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 15.10% a watan Janairun 2026 daga kashi N15.15% a watan Disamban 2025 a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, bisa kididigan farashin kayayyaki da aka fitar.
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ragu da kashi 127.4% a watan Janairun 2026, wanda ke nuna raguwar kashi 3.8% idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Hakazalika, NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 8.89% a watan Janairu daga kashi 10.84% a watan da ya gabata, idan ba’a manta ba dai hauhawar farashin kayayyaki ta karu zuwa kashi 15.15% a watan Disamban 2025, a cewar NBS.
Duk da raguwar farashin kayayyaki a watan Janairun 2026, ‘yan Najeriya sun ci gaba da kokawa kan hauhawar farashin kayayyaki a duk fadin kasar.
