Gobara ta tashi a kasuwar Singa ta Kano

0
1000503491
Spread the love

An samu rahoton barkewar gobara a Kasuwar Singa da ke kan titin Bello a Kano, lamarin da ya haifar da firgici tsakanin ‘yan kasuwa da mazauna yankin.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa gobarar ta fara ne da sanyin safiyar Litinin, inda gobarar ta bazu zuwa sassan kasuwar tare da lalata kayayyaki da sauran kayayyaki masu daraja mallakar ‘yan kasuwa.

Shaidu a wurin sun ce lamarin ya bukaci daukin gaggawa domin hana gobarar yaduwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *