Za mu ƙulla kasuwancin dala biliyan 5 da Najeriya – Shugaban Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na da burin ƙara yawan cinikayya da Najeriya zuwa dala biliyan 5, daga dala biliyan 2.
Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ziyarar aiki da Tinubu ya kai ƙasar.
Erdogan ya ce tuni aka fara tattaunawa domin cimma wannan buri, inda ya bayyana cewa Turkiyya na fitar da jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da injuna da ƙarafa da sinadarai zuwa Najeriya, yayin da Najeriya kuma ke fitar da ɗanyen mai da kayayyakin gona zuwa Turkiyya.
Erdogan ya kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, musamman ganin yadda matsalar ta’addanci ke barazana ga yankin Sahel da nahiyar Afirka baki ɗaya.
A nasa jawabin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Turkiyya bisa shirinta na haɗin gwiwa da Najeriya domin bunƙasa ‘yanci da zaman lafiya da wadata a duniya.
Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara, ciki har da na tsaro da na cinikayya da ilimi da kafofin watsa labarai da harkokin mata da jinƙai, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Turkiyya.
