Gwamnatin Sokoto za ta haramta ‘almubazzaranci’ yayin aure a jihar

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce gwamnatina za ta gabatar da dokokin haramta abin da ya kira almubazzaranci a lokacin aure a faɗin jihar.
Ahmad Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da masallaci da makamarantar zawiyyar Sheikh Aliyu Bunza da aka sabunta.
”Matakin ya zama wajibi saboda aydda ake samun ƙaruwar wahalhalun da ake ɗorawa mutanen da ke shirin yin aure ta hanyar tsara abubuwan da ba za zama wajibi ba, lamarin da ya sa matasa maza da mata da suka isa aure ke shan wahalar yin aure”, in ji gwamnan.
Gwamnan ya ce waɗannan wahalhalu na taimaka wa wajen ƙaruwar yawan marasa aure maza da mata a jihar.
”Wanda kuma hakan ke taimakawa wajen ƙaruwar rashin tarbiyya tsakanin matasa, waɗanda suka gaza yin aure saboda tsadar buƙatun da ake gabatarwa gabanin auren”, in ji gwamnan.
Matakin na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan wani bidiyon wata yarinya a jihar ya ɓulla da aka yi wa kayan lefe na gomman akwatina da motar hawa, lamarin da ya janye ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
