Gwamnatin Gombe ta haramta sana’ar jari bola

0
1000322696
Spread the love

Gwamnatin jihar Gombe ta haramta sana’ar jari bola a duka faɗin jihar, bisa dalilai na tsaro.

Gwamnatin ta amince da matakin ne bayan taron Majalisar Tsaro na musamman tare da manyan jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya domin nazarin sabbin ƙalubalen tsaro da faruwar wasu abubuwa masu tayar da hankali a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa haramcin zai fara aiki nan take kuma zai ci gaba har sai an tsara harkar a ƙarkashin shugabanci da kulawa ta musamman.

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta ce ta samu rahotannin satar kayan more rayuwa da kuma lalata kayan gwamnati da na makarantu, waɗanda galibi suke shiga hannun masu sana’ar bola jari.

Majalisar Tsaron ta nuna damuwa kan yadda rashin tsari da shugabanci na masu sna’ar ke haifar da wahalar sanya ido da kiyaye ayyukansu.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, nan gaba, za a kafa kwamitin aiwatarwa da sa ido kan harkar domin tabbatar da bin doka a dukkan ƙananan hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *