Allah ya yiwa Audu Ogbeh rasuwa.

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya karkara, Cif Audu Ogbeh rasuwa yana da shekaru 78 a duniya.
A wata sanarwa da iyalan Ogbeh suka fitar a ranar Asabar dinnan sun bayyana cewar dattijon ya rasu ne a ranar Asabar.
Sanarwan ta kara da cewa nan gaba kadan za’a bayyana lokacin jana’izar sa.
