Gwamnatin Adamawa ta karbi ‘ya’yan itatuwan dabino guda 400,000 don magance sauyin yanayi

Gwamnatin jihar Adamawa ta karbi nau’in itatuwan dabino guda 400,000 daga ƙungiyar Green Great World (GGW) a wani bangare na kokarin dakile tasirin sauyin yanayi a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli, Hon. Muhammad Sadiq, ya tabbatar da bayar da tallafin a Yola, inda ya bayyana cewa tsiron wasu nau’o’in tsiro ne masu yawan gaske wadanda suke tsirowa da girma a cikin shekaru hudu zuwa biyar, sabanin irin na gargajiya da suke daukar shekaru 20.
Kwamishinan ya bayyana kudirin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na kare muhalli, inda ya bayyana cewa gwamnatin ta kafa kwamitin kula da albarkatun kasa da muhalli na jiha (MIREMCO), wanda shi da kansa zai jagoranta.
Kwamitin ya tattauna batutuwan da suka shafi hakar ma’adinai da kuma shawo kan ambaliyar ruwa, ciki har da gano gidaje 84 da aka gina ba bisa ka’ida ba a kan magudanar ruwa a karamar hukumar Yola ta Kudu.
Dangane da zarge-zargen da ake yi na cire kudaden da kananan hukumomi ke bayarwa don gudanar da ayyukan tsaftar muhalli na wata-wata, Muhammad ya tabbatar da hakan amma ya nanata cewa abune da ya dace.
Ya bayyana cewa an saka harajin tsaftar muhalli na doka a cikin kason kowace karamar hukuma kuma an mika shi ga Ma’aikatar Muhalli don aiwatar da shirye-shiryen tsabtace muhalli.
Ya kara da cewa kungiyoyin da suka hada da bankuna da kamfanonin gine-gine, suma suna bayar da gudumawa ta hanyar daukar nauyin da ya rataya a wuyansu na zamantakewar al’umma don karfafa ayyukan tsaftar muhalli a jihar.
“Misali, idan har Naira miliyan 11 ne ake cirewa daga kananan hukumomin, ba komai bane, don haka muna neman tallafi daga wasu hanyoyi,” in ji Muhammad.
Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar Adamawa da su rungumi dabi’ar tsabtar muhalli mai kyau, yana mai jaddada cewa alhakin hadin gwiwa ya zama wajibi domin tabbatar da tsaftataccen iska da abinci ga kowa da kowa.
