A yanzu Najeriya ba ta da mai dauke da Cutar Ebola bayan fitar da mara lafiyar zuwa Switzerland — WHO

0
A yanzu Najeriya ba ta da mai dauke da Cutar Ebola bayan fitar da mara lafiyar zuwa Switzerland — WHO

A yanzu Najeriya ba ta da mai dauke da Cutar Ebola bayan fitar da mara lafiyar zuwa Switzerland — WHO

Spread the love

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ba ta da wani tabbataccen mai ɗauke da cutar Ebola, bayan an kwashe matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar tare da mijinta zuwa ƙasar Switzerland domin ci gaba da kula da lafiyarta.

Daraktan hukumar na yankin Afirka, Farfesa Mohamed Janabi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X.

Janabi ya bayyana cewa matar, wadda ‘yar asalin Switzerland ce, ta samu kulawa daga jami’an lafiya na Najeriya, inda suka yi nasarar shawo kan mummunan matakin farko na cutar tare da daidaita yanayin lafiyarta kafin a kwashe ta zuwa ƙasarta.

Ya kuma tabbatar da cewa mijinta, wanda shi ma ɗan ƙasar Switzerland ne kuma aka sanya cikin waɗanda ake bibiyar lafiyarsu saboda kusanci da mara lafiyar, yana tare da ita a yayin jigilar zuwa Switzerland.

Daraktan WHO na Afirka ya yaba wa gwamnatin Najeriya, ma’aikatan lafiya, likitoci da jami’an agajin gaggawa bisa irin gudummawar da suka bayar wajen kula da mara lafiyar da kuma shawo kan lamarin.

Ya bayyana nasarar a matsayin wata shaida da ke nuna ƙwarewar ƙasashen Afirka wajen tunkarar matsalolin lafiya, musamman idan aka samu haɗin kai tsakanin hukumomi da ma’aikatan lafiya.

Duk da wannan ci gaba, Janabi ya yi gargaɗin cewa har yanzu akwai buƙatar ci gaba da taka-tsantsan domin hana sake ɓullar cutar.

Ya ce hukumomin lafiya na Najeriya za su ci gaba da sa ido kan mutane 52 da suka yi hulɗa da mara lafiyar, yayin da hukumomin Switzerland za su kula da lafiyar matar tare da bibiyar mijinta, wanda shi ne mutum na 53 cikin waɗanda ake sa ido a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *