‘Jarumai na gaskiya’ – Matar Tinubu na taya murnar ranar malamai, ta bukaci a dauki mataki kan karancin su

0
1000202725
Spread the love

Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta ce malaman makarantu mutane masu daraja da suka cancanci yabo da ƙarƙafa gwiwa.

Remi ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da fitar domin murnar Ranar Malamai ta bana, inda ta yi kira da a ƙara ɗaukar malamai domin ɗalibai su samu ilimi mai inganci, sannan a kula sosai da haƙƙoƙinsu.

A cewarta, “malamai gwaraza ne gaskiya da suke taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma da ma gyara ƙasa.”

“Ƙarancin malamai matsala ce da ke buƙatar ɗauki na gaggawa domin idan aka ƙarfafa malamai ne wasu ma za su yi sha’awar shiga aikin mai matuƙar daraja.”

Ta ƙara da cewa, “a matsayina na tsohuwar malama, ina yabawa da ƙoƙarinku a wannan rana mai muhimmanci ta malamai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *