NAFDAC ta kulle kantunan ƴan China guda biyu a Abuja

0
1000110454
Spread the love

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta sanar da kulle wasu manyan kantunan kayan buƙatu guda biyu a babban birnin tarayya, Abuja da kuma wasu shagunan sayar da mayukan shafawa.

NAFDAC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a hafinta na X a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba, inda hukumar ta ce ta kulle manyan kantunan ne a yankin Jabi da kuma wasu shagunan sayar da mayukan shafawa guda takwas a kasuwar Wuse.

Sanarwar ta ce an rufe shagunan ne bisa saɓa dokokin kasuwanci da rarraba wasu kayayyaki bayan wasu kwastomomi sun kai ƙorafi a kuma bincike “ya tabbatar suna sayar da kayayyakin da ba suka saɓa dokokin rajista, kuma suke ɗauke da tambarin China.

“Hukumar ta ce hakan ya saɓa dokokinta, “domin dole ne a sanya tambari da turancin Ingilishi a duk kayayyakin a za a sayar a Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *