Ɗanwasan Real Madrid Reinier Jesus ya koma Brazil da taka leda

Ɗanwasan tsakiya na Real Madrid Reinier Jesus ya koma Atlético Mineiro ta Brazil da taka leda.
Saura shekara ɗaya kwantaraginsa ya ƙare a Madrid amma duk da haka Real ta cimma yarjejeniyar cinikinsa da Atletico.
Ɗan shekara 23 ɗin ya koma Real ne a watan Janairun 2020 kan yuro miliyan 30 daga Flamengo ta Brazil ɗin, amma bai taɓa buga wa babbar tawagar Madrid wasa ba.
An tura shi wasa aro sau huɗu zuwa Borussia Dortmund, da Girona, da Frosinone, da Granada.
Reinier ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara huɗu da Mineiro zuwa 2029, amma Real ce ke da alhakin samun rabin kuɗinsa idan Mineiro za ta sake sayar da shi nan gaba.
