Ƴanbindiga sun yi garkuwa da wani Ba’Armuke a birnin Yamai na Nijar

0
1000148769
Spread the love

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi gurkuwa da wani Ba’amurke a daren jiya a birnin Yamai.

Wasu majiyoyi ciki harda na tsaro sun tabbatar da RFI, Ba’amurken matukin jirgi ne mai shekaru 48 wanda ke gudanar da ayyukan jin kai tare da masu bishara.

Rahotanni na cewa wannan Ba’amurke mazaunin wata unguwar da ake kira Château 1 , kusa da Grand Hotel Bravia, a tsakiyar birnin Yamai.

Unguwace da akasari ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ke aiki a kasar ke zaune a can, saboda akwai tsaro na musamman, la’akari da cewa anguwa ce mai nisan ƙasa da mita 500 daga fadar shugaban ƙasa.

Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhaƙin garkuwa da Ba’amurken, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaron cikin gida da na waje a Nijar na ganawar gaggauwa kan wannan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *