Ƴanbindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 a Filato

Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindiga sun yi awon gaba da matafiya 28 daga garin Zak da ke yankin Bashar a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato.
Wani mazaunin karamar hukumar wanda ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce mutanen da aka sace, da suka haɗa da maza da mata da yara na hanyar su ta zuwa garin Sabon Layi ne domin halartar taron Maulidi a jiya Lahadi.
”Da safiyar Litinin ne mutane da ke bin hanyar suka ga mota a kan titi, motar wani shugaban al’ummar Zak. Bayan bincike ne aka gane ita ce motar da ke ɗauke da matafiyan,” in ji shi.
Wani mazaunin garin ya kuma shaida wa gidan jaridar cewa zuwa yanzu babu labarin inda mutanen suke.
