Ƙungiyar D’Tigress ta Najeriya ta lashe Gasar ƙwallon kwandon Afirka, FIBA.

0
1000053166
Spread the love

Ƙungiyar D’Tigress ta Najeriya ta kafa tarihin zama ta farko da ta taɓa lashe Gasar ƙwallon kwandon Afirka, FIBA sau biyar a jere.

Tawagar ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin lashe gasar, karo na bakwai a tarihi.

Wannan nasarar na nufin za su je Gasar ƙwallon kwando ta duniya da za a yi a 2026 a birnin Berlin.

Ƴan wasan Najeriyar sun kankane Gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015.

D’Tigress na komawa gida Najeriya daga birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast, inda za su haɗu da shugaban Najeriya Bola Tinubu don kai masa kofin da suka lashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *