Zulum ya jajantawa mutanen da suka fiskanci hare hare a Borno

0
1000051878
Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Darajamal da ke ƙaramar hukumar Bama domin jajanta wa ƴan’uwan aƙalla mutum 63 da ƴan Boko Haram suka kashe a daren Juma’a.

Daga cikin waɗanda aka kashe ɗin har da sojoji biyar da fararen hula 58 daga cikin waɗanda suka koma garin bayan ɗaukar tsawon lokaci suna gudun hijira.

A zantawarsa da menama labarai, gwamnan ya ce, “mun zo ne domin jajanta muku bisa abin da ya faru a Darajamal, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane da dama.

Lamarin nan abin takaici ne. Watanni kaɗan da suka gabata ne mutanen garin nan suka koma gidajen su, har sun ci gaba da gudanar da ayyukan su, amma kwatsam sai aka kai musu wannan hari na Boko Haram,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum 63, “ciki har da farareb hula da sojoji.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *