Zelensky ya gargadi Trump kan barazanar jiragen yakin Iran
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya gargadi shugaban Amurka, Donald Trump, cewa makamai masu linzami ba za su iya dakatar da yawan hare-haren jirage marasa matuka da Iran ke amfani da su ba.
Zelenskyy ya bayyana cewa Iran na amfani da dabarar tura jirage masu yawa lokaci guda domin kai hari, lamarin da ke da wahalar dakile wa ko da an yi amfani da manyan makamai na kariya.
Shugaban na Ukraine ya ce waɗannan jiragen duk da cewa ba su da tsada kamar makamai masu linzami, amma suna da haɗari saboda yawansu da sauƙin sarrafa su.
Ya ƙara da cewa idan aka tura su da yawa a lokaci guda, suna iya rikita tsarin kariyar samaniya na ƙasashe.
Zelensky ya jaddada cewa Ukraine ta riga ta samu ƙwarewa wajen yaƙar irin waɗannan hare-hare sakamakon yaƙin da take yi da Rasha.
A cewar shugaban na Ukraine, wannan wani muhimmin gargaɗi ne ga Amurka da sauran ƙasashe masu ƙarfi, inda ya nuna cewa dogaro da makamai masu tsada kaɗai ba zai wadatar ba wajen tinkarar wannan sabuwar barazana.
