Zanga-zanga ta ɓarke a Filato bayan harin Palm Sunday
Gwamnan Jihar Filato Caleb Mufwang
Mazauna Jihar Filato sun fito zanga-zanga bayan hare-haren da aka kai a ranar Palm Sunday, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Masu zanga-zangar sun nuna fushi da takaici kan yadda ake ci gaba da samun hare-hare ba tare da tsauraran matakan tsaro ba, inda suka bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin jama’a sun fito kan tituna duk da dokar hana fita, domin nuna rashin amincewarsu da halin da ake ciki.
Al’umma na ci gaba da kira ga hukumomi da su kawo karshen kashe-kashen tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
