Za mu zauna da masu zanga-zanga don magance buƙatunsu – Shugaban Iran

Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa na son zama da abin da ya kira ‘ainihin’ masu zanga-zangar domin magance matalolinsu.
Yayin wani jawabi da ya yi wa ƙasar ta gidan talbijin, Mista Pezeshkian ya ce maƙiyan Iran ne suka kitsa halin da ake ciki a ƙasar.
Mista Pezeshkian ya nuna bambanci tsakanin ainihin masu zanga-zanga da waɗanda ya bayyana da ”ƴanta’adda masu tayar da hargitsi”.
Gwamnatinsa na fuskantar matsin lamba don magance matsalolin tattalin arziki, wanda shi ne ya haifar da zanga-zangar ta yanzu.
Tun bayan fara zanga-zangar aka riƙa samun ƙarin kiraye-kirayen hamɓarar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci.
