‘Za mu tsananta hare-hare ta sama domin kakkaɓe ƴanbindiga’

Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da umarni ga kwamandojin da ke lura da jiragen yaƙi su tsananta hare-hare kan maɓoyar ƴanbindiga a ƙasar.
Aneke ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron da ya jagoranta tsakanin manyan kwamandojin da ke jagorantar rundunonin da ke yaƙi da ƴanbindiga a ƙasar
Taron ya tattauna sabbin dabarun da rundunar za ta ɓullo da su wajen kai hare-hare kan maɓaiyar ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Sanarwar bayan da taron da rundunar sojin saman ta fitar, ta ce a ganawar manyan dakarun an ɓullo da dabarun haɗin gwiwa tsakanin rundunar sojin saman da sauran rundunonin tsaron.
Matakin na zuwa ne mako guda bayan da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin shugabannin rundunonin sojin ƙasar.
