Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II

0
1000151499
Spread the love

Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin kakarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan.

Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta a cikin cocin St. George’s Chapel da ke fadar Windsor.

Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Harry ya kai ziyara shi kaɗai domin girmama mahaifiyarsa.

A halin yanzu dai abin tambayar shi ne ko Yarima Harry zai gana da mahaifinsa, Sarki Charles III, wanda ke fama da cutar daji, bayan shekaru suna fama da rigimar cikin gida.

Rabon Harry ya gana da mahaifinsa tun watan Fabrairu 2024, lokacin da ya yi gaggawar dawowa Ingila bayan ya samu labarin cewa sarkin mai shekara 76 na fama da jinya.

Yarima Harry, mai shekara 40, ya halarci bikin ba da kyaututtuka na WellChild a daren Litinin a birnin London, inda ake girmama jarirai da yaran da suka yi bajinta duk da nakasa ko rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *