‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin barayin shanu ne a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu da ake zargin barayin shanu ne da suka shiga Najeriya ba bisa ka’ida ba daga jamhuriyar Nijar.
Majiyoyi sun ce jami’an tsaron kan iyaka ne suka cafke wadanda ake zargin a ranar 25 ga watan Satumba da misalin karfe 6:15 na safe.
Ya ce rundunar ‘yan sintiri da ke a gidan Dankama Guard Post ta kama wadanda ake zargin a kauyen Duma da ke karamar hukumar Kaita.
“Wadanda ake zargin, Abubakar Dayyabu mai shekaru 40 da Sa’adu Zubairu mai shekaru 45, dukkansu ‘yan kauyen Jankuki a jamhuriyar Nijar, an same su da shanu biyu ba tare da wasu shaidu dake nuna nasu ne ba,” inji majiyar.
Ya kara da cewa an mika wadanda ake zargin ga jami’in da ke kula da ofishin ‘yan sanda na Dankama domin ci gaba da bincike.
