‘Yan sanda sun ceto yara biyar da aka sace a Adamawa

0
1000157702
Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake kyautata zaton an sace su daga Maiduguri na jihar Borno, aka kai su Adamawa.

Yaran dukkan mazauna garin Gwange a Maiduguri sun hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya, da Mohammed Alhassan.

A cewar rundunar, an yi nasarar ceto yaran ne a ranar 13 ga Satumba, 2025, lokacin da kwamandan yankin Mubi, ACP Marcos Mancha, bisa sahihan bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa wajen cafke yaran da aka gano suna yawo a kan titunan garin Mubi.

Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa wani Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange ne ya dauke yaran daga Maiduguri, wanda a halin yanzu ya gudu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa, CP Dankombo Morris, ya yabawa kwamandan yankin da tawagarsa bisa wannan samame da aka kai musu.

Ya ce an umarci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta dauki nauyin lamarin tare da tabbatar da kama wanda ake zargin.

Morris ya kuma ba da tabbacin cewa yaran za su sake haduwa da iyayensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *