‘Yan bindiga sun sace Liman da kansiloli a jihar Zamfara

Wasu ‘Yanbindiga sun sace kansiloli biyu da limamin wani masallaci a garin Tsauni da ke birnin Gusau na jihar Zamfara a arewacin Najeriya.
Kansilolin na wakiltar mazabun Gidan Goga da Tsibiri a karamar hukumar Maradun, an sace su da misalin karfe 8 na daren ranar Laraba a kusa da ofishin ‘yan sanda da ke yankin jim kadan bayan kammala sallar Magariba.
Shugaban karamar hukumar Maradun Honarabul Sanusi Gama Giwa, ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin da ta ce dykkansu ‘yan mazabar shi ne.
Giwa ya ce mutanen na hutawa a wurin wani mai saida shayi, lokacin da ‘yanbindigar suka far musu, tare da kwace wayoyin ‘yansandan da ke wurin da awon gaba da mutum 6, amma daga bisani sun sako uku tare da gaba da Limam da kansilolin biyu.
Rahotanni sun ce sun zo neman wani mutumin karamar hukumar Kaura amma da ba su gan shi ba sukai awon gaba da mutanen da ke wurin mai shayin.
