Yadda Tchiroma Bakary ya ɓulla a Gambia bayan ɓatan-dabo

Gwamnatin Gambia ta tabbatar da cewa Issa Tchiroma Bakary, jagoran ƴan hamayya a ƙasar Kamaru, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Oktoba ya isa ƙasar domin samun mafaka da tsaro.
A wata sanarwa da ma’aikatar watsa labaran ƙasar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce Bakary ya isa ƙasar ne a ranar 7 ga watan Nuwamba.
Wannan ne ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan ina tsohon jami’in gwamnatin ƙasar ta Kamaru yake.
“Ya iso ƙasarmu inda zai zauna na wani ɗan lokaci saboda tabbatar da tsaronsa a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan samar da matsaya mai kyau cikin diflomasiyya kan abubuwan da suka faru bayan zaɓen Kamaru,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
