Ya kamata a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da talauci a Najeriya – Atiku

0
20250601_134212
Spread the love

Tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana talauci a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo tsaiko ga cigaban duniya.

Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta a cikin jawabinsa na Ranar Yaƙi da Talauci ta Najeriya, inda ya ƙara a cewa abin takaici ne yadda Najeriya ta kasance gaba-gaba cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci.

A cewar Atiku, manyan abubuwan da suke jawo talauci sun haɗa da “jahilci da rashin tsaro da cututtuka,” in ji shi, sannan ya yi kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalar.

“Ya kamata gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki duk a taru a haɗa hannu domin yaƙi da talauci a Najeriya. Abin ban haushi ne a ce Najeriya muna cikin ƙasashen da aka fi talauci, shi ya sa nake kira da a ba al’ummar ƙasar muhimmanci domin magance matsalar nan ta talauci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *