Yaƙi na kara tsananta: Iran ta gargadi Amurka kan tura sojoji Gabas ta Tsakiya
Ƙasar Iran ta yi wa Amurka gargaɗi mai tsauri kan shirin tura ƙarin sojoji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda ta ce tana sa ido sosai kan duk wani motsi na sojojin Amurka a yankin.
Iran ta bayyana cewa duk wani ƙarin tura sojoji zai iya jefa su cikin haɗari, tare da cewa sojojin Amurka za su iya zama waɗanda hare-hare za su rutsa da su idan rikicin ya ƙara tsananta.
Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke shirin ƙara yawan dakarunta domin ƙarfafa matsayinta a yankin, sakamakon rikicin da ke ƙara kamari tsakaninta da Iran.
Masana sun nuna cewa wannan yanayi na iya ƙara haddasa tashin hankali, tare da barazanar rikicin ya rikide zuwa babbar faɗa idan ba a samu mafita ta diflomasiyya ba.
