Wasu ‘yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe mutane biyar a lokacin sallar asuba a Zamfara

A ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari a wani masallaci a unguwar Yandoto da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka kashe wasu mutane biyar a lokacin sallar asuba.

Shedun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa maharan sun far wa masallatan ne da sanyin safiya a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da sallah inda suka bude wuta kan jama’ar.
Lamarin da ya faru da misalin karfe 5:00 na safe, ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin, yayin da maharan suka kuma yi awon gaba da wasu masu ibada da ba a tantance adadinsu ba, inda aka tafi da su cikin dajin.

Daga bisani an gudanar da sallar jana’izar mutane biyar da aka kash, harin dai ya haifar da bacin rai a tsakanin al’umma, inda mazauna yankin suka yi kira ga hukumomi da su kara tsaurara matakan tsaro a Tsafe da kuma fadin Zamfara domin kawo karshen tashe-tashen hankula da ke ci gaba da faruwa.
