Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mai POS, sun kuma raunata wasu a Kano

‘Yan bindiga sun kashe wani matashin mai sana’ar POS tare da raunata mutane da dama a lokacin wani hari da suka kai a ƙauyen Sodawa, ta jihar Kano.
Wani mazaunin garin, Mallam Zaharaddin, ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da daddare a daren Lahadi.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigar an yi zargin ‘yan fashi da makami ne da suka bi sawun wanda aka kashe bayan ya cire kuɗin kasuwancinsa.
“Sun tare shi a kan hanyarsa suka bude masa wuta, suka kashe shi nan take,” in ji Zaharaddin.
“Bayan haka, sun ci gaba da harbi da kai hari a shaguna da ke kusa.”Daga baya jami’an tsaro sun isa wurin da abin ya faru suka kai waɗanda suka ji rauni asibiti don neman magani cikin gaggawa.
Ya ƙara da cewa ba wannan ne karo na farko da ‘yan bindiga suka kai hari a yankin ba, wanda ke kan iyaka da jihar Jigawa.
Ya ce mazauna yankin suna nuna tsoro da takaici, yana kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki mataki cikin gaggawa don kawo ƙarshen rashin tsaro da ke ƙaruwa a cikin al’ummarsu.
