Wani yaro dan shekara 16 ya kashe yadikkon sa yayin da wani matashin kuwa ya da6awa mahifinsa wuka a Adamawa.

0
1000038682
Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a halin yanzu tana gudanar da bincike kan wasu laifuka guda biyu na kisan kai da suka taso a rikicin cikin gida a kananan hukumomin Madagali da Gombi.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa lamarin na farko ya faru ne a gundumar Pallam da ke Madagali.

A cewar sanarwar, wani bincike na farko da aka gudanar ya nuna cewa wata arangama ta barke tsakanin mata biyu, Rhoda Anthony, mai shekaru 55, da Victoria Anthony, mai shekaru 36, dukkansu sun kasance matan Anthony Pallam.

A yayin rikicin, dan Victoria, Ijai Anthony, mai shekaru 16, an ruwaito cewa ya bugi kishiyar mahaifiyarsa, Rhoda Anthony, a kai da itace, wanda ya sa ta fadi, bayan samun rahoton, jami’in ‘yan sanda Madagali ya garzaya wurin da lamarin ya faru da gaggawa, inda aka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa Cottage Hospital Madagali, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarta yayin da take karbar magani.” Ya ce an tsare wanda ake zargin da mahaifiyarsa a gidan yari yayin da ake ci gaba da bincike.

Sanarwar ta kara da cewa, “A wani mummunan lamari makamancin haka da ya afku a gundumar Fotta da ke karamar hukumar Gombi.” Rundunar ‘yan sandan ta samu rahoton tashin hankali cewa wani mai suna Idi Buba ya kai wa mahaifinsa mai suna Buba Jelli hari ta hanyar daba masa wuka a wuya da bayansa, biyo bayan rikicin cikin gida.

Nan take aka garzaya da wanda aka kashen zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke Fotta, inda ya rasu a lokacin da yake jinya.

Nguroje ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin a wurin da lamarin ya faru, kuma an kuma gano wukar da aka yi amfani da shi, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, CP Dankombo Morris, ya yi Allah wadai da irin wadannan ta’addanci musamman wadanda suka shafi ‘yan uwa.

Ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kasance masu kamun kai, su guji daukar doka a hannunsu, da kuma neman hanyar lumana wajen warware rikici.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *